
Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON ta sanar da shirin fara aikin jigilar alhazan Najeriya na hajjin bana a ƙasar Saudiyya.
Anofiu Elegushi kwamshinan ayyukan yau da kullum na hukumar shi ne ya bayyana haka a ranar Litinin a wurin sanya hannu da kamfanonin jiragen saman da za su ɗauki alhazan Najeriya a bana.
Jiragen da za suyi jigilar a bana sun haɗa da FlyNas, Air Peace, Max Air, da Umza Air Limited.
A cewar Elegushi ƙasar Saudiyya za ta buɗe sararin samaniyarta domin fara saukar alhazai a ranar 29 ga watan Afrilu a yayin da aka shirya jirgin farko daga Najeriya zai ta shi ranar 6 ga watan Mayu.
Ya ƙara da cewa NAHCON na aiki kafada da kafada da hukumomin aikin hajji na jihohi wajen jigilar alhazan kimanin 75,000 daga jihohi daban-daban na Najeriya.