
Hukumar Aikin Hajji ta Kasa, NAHCON ta sanar da naira miliyan ₦8.5 a matsayin kudin wucin gadi na kujerar aikin hajjin shekarar 2026.
A wata sanarwa mataimakiyar daraktan sadarwa ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce an sanar da kudin ne bayan da aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a aikin hajji kan yadda aikin hajji na shekarar 2025 ya gudana.
Usara ta ce cikakken kudin kujerar zai tabbata ne bayan an kammala tattaunawa kan duk wasu yarjejeniyoyi na kwangilar ayyukan da za a yiwa alhazan a kasa mai tsarki.
Ta ce Najeriya za ta cigaba da rike kasonta na kujera 94,000 da hukumomin kasar Saudiyya suka ware mata a Hajjin 2025 haka ma hukumomin alhazan jihohi su ma rabon kujerarsu zai kasance kamar yadda suka samu a shekarar da ta wuce.
Ta ruwaito shugaban hukumar, Abdullahi Saleh Pakistan na godewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan gudunmawar da ya bayar wajen samun nasarar aikin Hajjin.