
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce ta kammala kwashe alhazan jihohin Kogi, Imo, Oyo da kuma Abia.
A wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, Fatima Usara mataimakiyar daraktan yada labarai ta hukumar ta ce an samu cigaba sosai a aikin kwashe alhazan na bana idan aka kwatanta da na shekarar da ta wuce.
Usara ta ce kawo hukumar ta kwashe kaso 19 cikin dari na maniyatan aikin hajjin na bana a cikin kwanaki uku kacal da fara aikin jigilar alhazan mai makon kaso 9 da aka yi a kwanaki uku a shekarar 2024.
” kamfanin jiragen Air Peace ya kammala kwashe alhazan jihar Oyo inda aka kwashe jumullar alhazai 1083 aka kai su Saudiya lafiya,” a cewar sanarwar..
“Imo da Abia an kammala kwashe alhazan su sai da wasu kalilan da basu zo ba lokacin da aka kaddamar da aikin kwashe alhazan kuma za a saka su a wani jirgin anan gaba,”
Usara ta ce kamfanin jirgin saman Umza zai fara aikin kwashe alhazan jihar Kaduna a ranar 14 ga watan Mayu.