Na bi tsarin mulki wajen yi wa Joshua Dariye da Jolly Nyame afuwa

Fadar shugaban kasar Najeriya ta kare matakinta na yi wa wasu tsofaffin gwamnonin kasar wadanda ke tsare a gidan yari saboda cin hanci da rashawa afuwa.

Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari ya yi wa gwamnonin – Joshua Dariye da Jolly Nyame – afuwa ne saboda matsalar rashin lafiya bayan an duba yanayin da suke ciki.

Ya ce shawarar da majalisar magabata ta kasar ta bayar na a yi wa tsofaffin gwamnonin da wasu mutum 157, “hukunci ne da aka yanke cikin nutsuwa, kuma doka ta amince da hakan ba don cimma wata manufar siyasa ba.”

Duka gwamnonin dai na zaman gidan kaso ne bayan fuskantar shari’ar cin hanci da rasha da aka yi musu, kuma kotun koli ta yanke musu hukunci.

‘Yan Najeriya da dama dai sun yi ta Allah-wadai da wannan mataki, suna cewa, nawa ne masu fama da rashin lafiya da ke zaune gidan yarin ba a yi musu afuwa ba sai wadannan.

Ka zalika wasu na sukar cewa akwai wadanda suka fi su shekaru a zaune a gidan, wadanda wasu ko shari’a ba a yi musu ba.

A cikin sanarwar Malam Garba Shehu ya ce idan Buhari bai yi wa wadannan dattijai gafara ba, za a rika yi masa kallon mutum mara tausayi.

More from this stream

Recomended