Ba baƙon abu ba ne don an haifi yaro da haƙori a bakinsa—in ji masana lafiyar yara

Likitocin kula da lafiyar yara sun ce jariran da ke da hakora daya ko biyu a lokacin haihuwa hakan ba baƙon al’amari ba ne.

Wannan magana ta kawar da tsoro, tatsuniyoyi da suka daɗe, da rashin jin daɗin iyaye da ’yan uwa a lokacin da aka haifi jariransu da haƙora.

Sun hana iyayen irin wadannan yaran cire hakoran, inda suka yi gargadin cewa cirewar na iya kawo cikas ga ci gaban da ya dace da kuma hakora.

Wani bincike da Bankole O et al ya yi kan kore tatsuniyoyi da ke da alaƙa da haƙoran yaran da ake haihuwa ya gano cewa ba tare da la’akari da zamantakewar al’umma ba, ‘yan Nijeriya sun yi imani da la’antar jarirai masu haƙora a lokacin haihuwa.

A wajen Najeriya, irin wadannan jariran an yi imani da cewa su ‘yan iska ne ko dodanni kuma hakoran sun kasance alama ce ta alfarma da kuma alamar shaidan.

A sakamakon haka, iyaye, ’yan’uwa, da kuma wasu ma’aikatan jinya, kamar yadda rahoton ya bayyana, yawanci sukan nace a cire haƙoran.

More News

Jarumin Nollywwood, Mr. Ibu, ya rasu

Jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da "Mr Ibu", ya rasu yana da shekaru 62. Emeka Rollas, shugaban kungiyar Actors Guild of Nigeria,...

Miyetti Allah ta nemi a cafke Sunday Igboho saboda barazanar yaƙar Fulani

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ta yi kira da a damke wani dan kabilar Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi...

Daurawa ya yi murabus daga muƙamin shugabancin Hisbah a Kano

Sheikh Aminu Daurawa ya yi murabus daga muƙaminsa na Shugaban Hisbah na Jihar Kano. Malamin yace ya yi iya kokarinsa wajen gyaran tarbiyar matasan Kano...

Tirkashi: Matashi ya yi tattaki tun daga Gombe har Abuja

Wani direban mota mai shekaru 21 daga jihar Gombe, Suleiman Rabiu, ya yi tattakin sama da kilomita 700 domin nuna yabonsa ga Hafsan Hafsoshin...