Mutumin da ya ya fadi zabe a Indiya har sau 24 amma bai karaya ba

Vijayprakash Kondekar

Hakkin mallakar hoto
Omkar Khandekar

Alamar dan takara Kondekar ita ce takalmin boot, kuma kirarinsa shi ne “Jama’a ku zabi boot”

Dukkan zabukan da aka yi a Indiya na da wasu ‘yan takara masu zaman kansu da ke tsaywa takara, kuma duk da cewa akwai babban kalubale a gabansu, ba sa karaya.

Wannan ne labarin irin wannan dan takarar mai suna Vijayprakash Kondekar, mutumin da kawo yanzu ya fadi zabe sau 24 amma bai saduda ba.

A birnin Pune da ke yammacin kasar ta Indiya, kuma a yankin Shivaji Nagar, da wuya ka sami mutumin da ya fi Mista Kondekar farin jini.

Dattijon mai shekara 73 da haihuwa, ya shafe wata biyun da suka gabata yana zagayawa mazabarsa domin ya sami goyon bayan masu jefa kuri’a su zabe shi.

Ya ce: So nake in jawo hankalin jama’a cewa ba sai an shiga jam’iyyar siyasa ne za a iya samun nagartacciyar demokradiyya a kasa mafi girman mulkin demokradiyya ba.”

“Ina kuma son kasar nan ta saba da ‘yan takara masu zaman kansu, domin ita ce hanyar tsaftace siysasar kasarmu daga handama da babakeren da ya dabaibaye ta,” inji shi.

Mista Kondekar na neman a zabe shi ya wakilci mazabar majalisar kasa a zaben ranar 23 ga watan Afrilun bana.

Zabe a Indiya gagarumin aki ne, inda tun ranar 11 ga watan Afrilu aka fara kada kuri’a, amma sai ranar 23 ga watan Mayu za a kirga kuri’u bayan an yi zabukan a matakai bakwai a fadin kasar.


Indiya na da dubban jam’iyyun siyasa, kuma kowacce na da alamarta

Mista Kondekar dan takara ne mai zaman kansa, kuma yana fatan zama Firai minista wata rana.

Ya ce idan ya zama firai minista, zai rika bai wa kowane dan Indiya Rupee 17,000 (wato dalar Amurka 245). A ganinsa, wannan abu ne mai sauki idan gwamnati za ta rage hidimar da take yi a wasu sassa na mulkin kasar.

Har zuwa shekarun 1980, yana aiki ne a kamfanin samar da wutar lantarki a Maharashtra. Amma yanzu ana iya ganinsa yana yawo a Pune, inda yake tura wata keken daukar kaya da ya makala wa wani allon talla a jiki.

Mutanen birnin sun ce a da ya kan rubuta a allon cewa yana neman tallafin kudi daga al’umma, amma tallafin da bai zarce dalar Amurka daya ba kacal.

Amma yanzu taken da ya rubuta a allon shi ne “Nasara ga takalmi” – wadda shi ne alamar da hukumar zabe ta Indiya ta ba Mista Kondekar.

Mutane da dama kan fashe da dariya idan suka gan shi yana yakin neman zabe. Wasu kuma na daukar batun tamkar na barkwanci ne. Musamman idan aka gansa yana yawo a cikin rana a wannan lokaci mai zafin sanye da wani farin gajeren wando da mayafi a bisa kafadarsa.

Amma da sun ji labarinsa – cewa ya tsaya takarar mukamai na siyasa fiye da 24 – mukamai tun daga matakin kananan hukumomi zuwa na majalisar kasa, sai kaga suna jinjina masa.

Yana cikin tsirarrun ‘yan takara da ke neman a zabe su a zabukan kasar ta Indiya a bana. A shekarar 2014, ‘yan takara uku ne su kayi nasara aka zabe su cikin guda 3,000 da suka tsaya takara.

More from this stream

Recomended