
Segun Olowookere, wani mazaunin jihar Osun wanda aka yanke masa hukuncin kisa saboda zargin satar kaza da ƙwai a shekarar 2010 ya fito daga gidan yari.
A ranar 26 ga watan Disamba ne, Ademola Adeleke gwamnan jihar Osun ya yi afuwa ga ɗaurarru 53 ciki har da Olowookere.
Matakin da gwamnan ya ɗauka ya biyo bayan wata tattaunawa da ta karaɗe soshiyal midiya inda jarumar Nollywood Biola Adebayo ta tattauna da iyayen Olowookere a ciki su ka yi iƙirarin cewa wasu ƴan sanda sun kama ɗan nasu ba bisa ka’ida ba.
Mahaifinsa mai suna Olarewaju ya yi zargin cewa wani DPO na ƴan sanda ne ya buƙaci a biya kuɗi kafin a sake shi inda gaza biyan kudin ya jawo aka tura shi gidan yari.
A wani fefan bidiyo da jarumar ta fitar ranar Litinin ya nuna ta a bakin gidan yarin Ƙiriƙiri tare da Olowookere inda take godewa gwamnan jihar dama sauran ƴan Najeriya kan gudunmawar da suka bayar wajen fitar da shi daga gidan yari.