Mutum miliyan 2 za su yi aikin Hajjin bana

[ad_1]

Mutum miliyan 2 za su yi aikin Hajjin bana

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutum miliyan 2 za su yi aikin Hajjin bana

Kimanin mutum miliyan biyu ake sa ran za su halarci kwanakin aikin hajjin bana a kusa da cikin Makkah da ke kasar Saudiyya.

Aikin Hajjin na bana ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke kara fadada ikonta a duniya – kuma na baya-bayan nan shi ne rikicinta da kasar Kanada – inda matashin yarima mai jiran gado ke kawo sauye-sauye na siyasa da zamanantarwa a kasar.

Muhimmancin aikin Hajji ga musulmin duniya da yawansu ya kusa mutum biliyan biyu abu ne da baya sauyawa, amma yadda kasar Saudiyya ke shirya shi na sauyawa.

Karbar bakin alhazai zuwa kasar abu ne da ke ba hukumomin daular ta Saudiyya da mahukuntanta dumbin alfahari.

Amma ba shakka gudanar da wannan muhimmin aiki mai gagarumin sarkakiya na bukatar hangen nesa matuka- shi ya sa akan sami matsaloli da suka hada da rasa rayuka da dukiyoyi akai akai.

Kasar Saudiyya ta fadada wuraren aikin Hajjin fiye da wani lokaci a cikin tarihi.

Kuma a bana suna bayyana yadda fasaha da kimiyya ke taimakawa wajen saukaka ayyukan Hajjin.

Da misali kasar ta samar da manhajar yin tarjama daga harshen Larabci zuwa wasu harsunan duniya da kuma na bayar da taimako ga marasa lafiya, kuma a karon farko, mahajjata za su ga mata na tukin mota a bisa titunan kasar ta Saudiyya.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...