Mutum hudu sun sake kamuwa coronavirus a Najeriya

Kwayar cutar covid-19

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Hukumar hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce wasu mutum hudu sun sake kamuwa da coronavirus a kasar.

A cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter, NCDC, ta ce uku daga cikin mutum hudun a birnin Legas suke gudan kuma a Abuja babban birnin tarayyar Najeriyar.

Kazalika mutum daga cikin mutum hudun sun dawo Najeriya ne daga tafiyar da suka yi zuwa kasashen waje.

Ya zuwa yanzu dai wadanda suka kamu da annobar ta coronavirus sun kai arba’in a Najeriya.

  • Coronavirus: Lewandowski ya bada gudunmuwar Euro miliyan daya
  • Corona: Farashin man goge hannu da takunkumin rufe fuska sun tashi a Lagos

Tuni dai biyu daga cikinsu suka warke, yayin da mutum guda kuma ya mutu.

Ci gaba da yaduwar da coronavirus din ke yi ya sanya gwamnatin tarayyar Najeriyar da ma gwamnatoci na jihohi sun dauki matakan dakile yaduwar ta.

Daga cikin matakan da aka dauka a kasar har da dakatar da dukkan zaman shari’a da kotunan kasar ke yi, sai dai a kan lamari na gaggawa saboda fargabar cutar COVID-19.

Ita kuwa gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriyar, haramta kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira tsawon mako hudu.

A jiahar Kano kuwa, gwamnatn jahar ce ta haramta dukkan wani taron jama’a a fadin jahar, a wani matakin na dakile cunkoson al’umma dan kaucewa kamuwa da cutar.

Zamfara kuwa umarnin rufe dukkan hukumomi gwamnatin jahar ta yi domin kauce wa kamuwa da coronavirus.

Gwamnatin jihar Neja kuwa sanar da sanya dokar hana fita daga karfe takwas na safe zuwa takwas na dare ta yi.

More from this stream

Recomended