Mutum Hudu Sun Rasu Ciki Har Da Wanda Ya Kammala Karatun Likita A Kasar Chana Sakamakon Hadarin Mota A Katsina – AREWA News

INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN

Da marecen jiya Asabar ne, aka yi wani mummunan hadarin mota akan hanyar Dutsinma zuwa Katsina, da niyyar zuwa zumunchi garin Dutsinma, wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutum hudu, har da matasa biyu cikin su har da wanda ya karanto aikin Likita a kasar China, yana shirye-shirye fara tafiya bautar kasa, Allah ya amshi rayuwarsa, Dr. Sadiq Yahaya Zakka, da suke zaune a unguwar Lambuambun Khadija cikin birnin Katsina da kuma Auwal Shehu Dan Faranshi, da ke zaune a unguwar Unwala cikin garin Katsina. Dukkan su matasane abokan juna.

Majiyar mu ta ce hadarin ya faru ne jiya da misalin karfe biyu zuwa ukku na ranar Asabar, dukkan su sun kone kurmus, akwai Fahad da ya tsira da ranshi, yanzu haka yana kwance a asibitin kashi da ke Katsina ya samu kariya da dama. Wutar ta dauki tsawon lokaci tana ci. Wasu kuma na cewa mota biyu ce suka yi taho mu gama kuma duk suka kama da wuta, idan an baro gari ‘Yar Gamji.

A yau za a yi jana’izarsu kamar yadda addinin musulunci ya shimfida.

Allah ya jikansu da rahama!

More from this stream

Recomended