
Mutum daya aka bada rahoton ya jikkata a wata fashewar wani abu da tsakar ranar Litinin a wurin hawa motar haya dake kan babbar hanyar Mararaba zuwa Nyanya a birnin tarayya Abuja.
Wata gajeriyar sanarwa da rundunar sojan Najeriya ta fitar ta ce fashewar ta faru ne wurin sauka da hawa ababen hawa dake kallon barikin sojoji na Mogadishu Cantonment dake Asokoro.
Rundunar sojan ba ta bayar da cikakken bayani ba kan lamarin amma ta ce tuni aka shawo kansa.
Josephine Adeh mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce jami’an sashin kwance bom na rundunar sun gaggauta isa wurin bayan da suka samu labarin fashewar.
Adeh ta ce tuni aka fara bincike domin gano musabbabin fashewar da kuma wane irin nau’in abu ne ya fashe.
Ta ce mutum daya namiji ya jikkata a fashewar kuma yana can yana samun kulawar likitoci a asibiti.