Mutum 25 sun mutu a hadarin mota a Bauchi | BBC news

Babban sifeton 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu

Hakkin mallakar hoto
Nigeria Police Force

Image caption

Babban sifeton ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu

Akalla fasinja 25 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon wani mummunan hadarin mota da ya afku a kauyen Gubi da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano.

Hadarin dai ya hada da mota kirar Toyota Hammer mai dauke da mutum 22 da ta yi taho mu gama da motar bas kirar J5 mai dauke da wasu fasinja hudu da kuma shanu 20.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ce ta sanar da hakan cikin sanarwar da ta fitar dauke da sa hannun kakakinta, DSP Kamal Datti Abubakar, inda ta ce fasinjan su 26 sun samu kuna a jikinsu.

Jami’an tsaro ne da wasu ‘yan kishin kasa suka agaza wajen kwashe mutanen daga wajen da hadarin ya faru, inda kuma aka mika su asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa domin samun kulawar likitoci.

Sai dai kuma likitoci sun tabbatar da mutuwar 25 daga cikinsu bayan da aka isa asibitin yayin da guda daya a cikinsu ya ke samun kulawa.

Kawo yanzu, mutum hudu cikin wadanda suka mutu aka iya ganewa daga cikin motar J5 kuma tuni aka mika wa iyalansu gawarwakinsu domin yi masu sutura.

Su kuma sauran 21 da ke cikin motar Toyota aka gaza gane su.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Bauchi ta kuma ce tana kan gudanar da bincike domin gano musabbabin hadarin.

More from this stream

Recomended