Mutum ɗaya ya mutu wasu sun jikkata a hatsarin motar tankar gas

Mutum ɗaya ya mutu a yayin da wasu biyu suka jikkata bayan da wata tankar gas tayi bindiga ta kama da wuta a Ita-Oshin dake kan titin Lagos-Abeokuta.

Da ta ke tabbatarwa da ƴan jaridu faruwar lamarin mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC a jihar Ogun, Florence Okpe ta ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 04:10 na ranar Asabar.

Ta ce mutane shida dukkanninsu maza su ne hatsarin ya rutsa da su.

Ta ƙara da cewa nan take yaron motar ya mutu.

Mai magana da yawun FRSC ta cigaba da cewa birki ne ya shanyewa motar tankar gas inda ta ƙwacewa direban ta daki gefen titi ta kuma kama da wuta.

Har ila yau hatsarin ya jawo konewar wasu motoci da kuma gine-gine dake kusa da inda lamarin ya faru.

More from this stream

Recomended