Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Indonesia ta ce a kalla mutum 832 ne suka rasa rayukansu sakamakon mummunar girgizar kasa da bala’in tsunami da ya afkawa tsibirin Sulawesi na kasar.
Rahotanni sun ce baraguzan gini sun rufe wasu mutanen da dama.
Masu aikin ceto na ta tona wuraren da abin ya faru domin neman mutanen da ba a gani ba a Palu.
Shugaban hukumar agajin gaggawa na kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, yanzu abinda suke bukata shi ne babban injin da zai taimaka musu wajen kwashe baraguzan ginin da suka rushe, don su samu gano mutanen da ake nema.
Mataimakin shugaban kasar Jusuf Kalla, ya ce adadin wadanda suka rasa rayukansu zai iya haura na yanzu kasancewar har yanzu ana ba a gano wasu mutanen ba.
Ana nuna damuwa a kan halin da garin Donggala ke ciki inda har yanzu ba a kai ga gano illar da girgizar kasar ta haifar ba.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta kiyasta cewa mutane fiye da miliyan daya da rabi ne girgizar kasar ta shafa.
Tuni dai shugaban kasar Joko Widodo, ya ziyarci birnin Palu domin gane wa idanunsa irin bala’in da girgirzar kasar ta haifar.
Igiyoyin ruwa ne suka yi tunkoro har zuwa tsayin mita uku hakan ya sa ruwa ya shafe tsibirin Sulawesi.
Hotunan bidiyon da aka sanya a kafafan sada zumunta sun nuna yadda mutane ke ta kururuwa tare da tserewa a cikin dimuwa.
Dubban gidaje da asibitoci da ote-otel da kuma shaguna ne suka rushe sakamakon girgizar kasar.
Ruwan sha ya yi karanci a wuraren da girgizar ta afku, yayin da wadanda lamarin ya shafa kuma ke fakewa a filin Allah Ta’ala saboda rashin inda za su tsugunna.