Mutane uku sun mutu a hatsarin mota

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos,LASEMA ta ce mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya haɗa da manyan motocin ɗaukar kwantena.

A cikin wata sanarwa, Olufemi Oke-Osanyintolu babban sakataren dindin na hukumar ya ce hatsarin ya faru a mahadar titin 174 Battalion, PZ a Ikorudu.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa motar dake ɗauke da kwantena mai tsawon ƙafa 20 dake cike da kaya ta ƙwace daga hannun direban ta sauka daga titin taje ta daki wata motar kwantena dake ajiye ita faɗa kan wani shago.

Oke-Osanyintolu ya ce mutane biyar ne suka makale a kasan motar kwantenar dake ajiye inda aka samu nasarar ciro gawar mutane uku , mutum ɗaya a raye a yayin da ake cigaba da neman mutum na uku.

More from this stream

Recomended