Mutane uku da shanu 319 aka kashe a jihar Plateau

Rundunar ƴansandan jihar Plateau ta tabbatar da mutuwar mutane uku da kuma shanu 319 a wasu hare-hare da aka kai daban-daban a lardin Miango dake karamar hukumar Bassa ta jihar.

A wata sanarwa da Tyopev Terna mai magana da yawun rundunar yansandan jihar ya fitar ta bayyana cewa Fulani makiyaya biyu ne suka bata ya yin kai harin.

Terna ya ce harin akan Fulani makiyaya na zuwa ne kwana guda bayan da wasu yanbindiga da ba a san ko suwaye ba suka kashe mutane uku a ƙauyuka daban-daban dake karamar hukumar.

Ya kara da cewa an jikkata wata jaririya yar wata 7 a harin inda take asibiti tana samun kulawa.

Mai magana da yawun rundunar ya ce tuni aka tura wata tawaga domin bincikowa tare da ceto makiyayan da suka bace ya yin da ake cigaba da bin sawun waɗanda suka kai harin.

More from this stream

Recomended