Mutane da suka mutu a harin Gwoza sun ƙaru zuwa 18

Yawan mutanen da suka mutu a harin ƙunar baƙin wake a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno sun ƙaru ya zuwa mutane 18.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno, Barkindo Saidu shi ne ya tabbatarwa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN haka ranar Lahadi.

Sa’idu ya ce mutanen da suka mutu sun haɗa da maza da mata manya da kuma ƙananan yara.

A ranar Asabar ne dai wasu ƴan ƙunar baƙin wake suka tayar da bama-bamai biyu a garin na Gwoza a lokuta daban-daban.

Sa’idu ya ce ” mutane 19″ sun jikkata sosai a yayin da wasu 23 ke jiran rakiyar jami’an tsaro ya zuwa asibitin sojoji.

Ya ƙara da cewa yanzu haka yana shirya yadda za ayi amfani da jirgi mai saukar ungulu ya zuwa garin.

More from this stream

Recomended