Mutane da dama ne da kawo yanzu da ba a san yawansu ba ake fargabar sun mutu a wani turmutsutsu da aka yi a garin Okija dake jihar Anambra.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar a yayin wani taron rabon shinkafa.
Yawancin mutanen da abun ya rutsa da su da yawancin su mata ne.
Wasu fefayen bidiyo da aka watsa a shafukan soshiyal midiya sun nuna gawarwakin mutane a barbaje a ƙasa..
Wasu daga cikin mutane da abun ya rutsa da su an garzaya da su asibiti dake kusa.
Charles Aburime, mai magana da yawun gwamnan jihar Anambra ya tabbatar da faruwar lamarin.
Aburime ya ce gwamnatin jihar na cigaba da bibiyar batun nan gaba kuma kaɗan za ta fitar da sanarwa.