
Mutanen da kawo yanzu ba a tantance yawansu ba ne suka mutu a wata gobarar tankar mai da ta faru a jihar Ogun.
Hatsarin gobarar ya faru ne da misalin karfe 01:00 na daren ranar Juma’a.
Mai magana da yawun hukumar TRACE dake tabbatar da bin kaidojin tuki a jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi ya ce motar dake dauke da litar mai 33000 ta kife akan titi sakamakon gudun wuce ka’ida da take tare da zubar da man dake ciki da hakan ya haifar da tashin gobara.
Akinbiyi ya ce lamarin ya faru akan titin Abeokuta-Kobape-Siu- Sagamu.
Ya kara da cewa gobarar ta kuma watsu inda ta kone wasu ƙarin motoci tare da turakun wutar lantarki.
Hatsarin motar tankar mai abu ne da yake yawan faruwa akan titunan Najeriya.