Mutane da dama sun maƙale cikin baraguzan bene mai hawa uku da ya ruguzo a Lagos

Mutane da dama aka bada rahoton sun maƙale a cikin baraguzan wani ginin bene mai hawa uku da ya ruguzo dake layin Orumeta a yankin unguwar Ojudu-Berger dake jihar Lagos.

Rahotanni sun bayyana cewa ginin wanda ake tsaka da ginawa ya ruguzo da misalin ƙarfe 08:00 na safiyar ranar Asabar inda aka ceto mutane biyar daga ciki.

Ginin na ɗauke da wani wurin sayar da abinci a ƙasansa.

Da yake magana da manema labarai a wurin da lamarin ya faru babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos LASEMA ya ce masu aikin ceto za su tone har ƙasa domin zaƙulo wadanda suka maƙale.

Wani dake zuwa gidan abincin akai-akai ya faɗi cewa ginin ya dade yana nuna alamar gazawa amma sai da masu ginin suka ƙara masa hawa ɗaya ya koma uku.

Wani mazaunin unguwar mai suna, Abiola David ya ce ginin ya binne wata mota da aka ajiye a harabar wurin dake ɗauke da mai ita da kuma ɗansa a lokacin da ya ruguzo.

More from this stream

Recomended