
Mutane da dama ake fargabar sun riga mu gidan gaskiya biyo bayan wani mummunan hatsarin mota da hada da wasu tankokin man fetur da kuma kananan motocin kirar Golf unguwar Dan Magaji dake garin Zariya.
Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 08:30 na safiyar ranar Litinin a kusa da makarantar gidauniyar Rochas dake kan titin Zariya zuwa Kano.
A cewar wasu shedun gani da ido mutum guda ne ya samu nasarar tsira da ransa daga cikin motocin da abun ya rutsa da su.
Kokarin da mutane su ka yi na kai dauki wurin domin ceto wasu daga cikin mutanen da suke cikin motocin ya gaza cin tura.
Kawo yanzu dai rundunar yan sandan jihar Kaduna ko kuma hukumar FRSC dake kare afkuwar hadura a titunan Najeriya basu fitar da wata sanarwa ba kan faruwar hatsarin.