
Mutane biyu aka tabbatar da sun mutu a yayin da wasu shida suka ji mummunan rauni bayan da wani ginin bene hawa uku ya ruguzo a unguwar Odoriwu dake jihar Lagos.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos LASEMA ta ce ta tura jami’anta ya zuwa wurin daga ofisoshinta dake Lekki da kuma Cappa bayan da ta samu kiran kai ɗaukin gaggawa da misalin ƙarfe 02:25 na ranar Laraba.
Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu babban sakataren dindin na hukumar ta LASEMA ya ce an zaƙulo gawar mutane biyu maza daga cikin baraguzan ginin.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka jikkata sun samu taimakon farko a wurin kafin a ɗauke su ya zuwa Asibitin Mariam domin cigaba da samun kulawa.
Ya ƙara da cewa ba a san musabbabin ruguzowar ginin ba inda ya ƙara da cewa za a cigaba da bincike.