Mutane biyu sun mutu a rikici tsakanin sojoji da ƴan sanda a jihar Nasarawa

Rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa ta ce mutane biyu aka tabbatar da sun mutu bayan wani faɗa da aka yi tsakanin sojoji da ƴan sandan konsitabulari a kasuwar Agyaragu dake ƙaramar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

A wata sanarwa ranar Lahadi, Rahman Nansel mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:30 na rana lokacin da ake gudanar da bincike kan satar babur.

Nansel ya ce bayan kai rahoton satar ne  jami’an ƴan sanda da taimakon konsitabulari na ofishin ƴan sanda na Jenkwe sun kama wani da ake zargi a kasuwar Agyaragu.

Ya ƙara da cewa a lokacin da suka ɗauke shi zuwa ofishin ƴan sanda sai wani soja da aka ce ya dawo hutu daga jihar Borno ya nemi ya hana kamen inda ya farma ƴan sandan.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan  ya ce sojan ya ciro wuƙa inda ya cakawa konsitabularin.

“A ƙoƙarin kare kai an murɗe sojan inda aka yi amfani da wukar ta sa akansa. Dukkansu sun samu raunuka daga bisani aka tabbatar da mutuwar sojan da aka jikkata,” a cewar sanarwar.

Ya ƙara da cewa bayan rikicin ne wasu dandazon matasa suka taru suka ƙona ofishin ƴan sandan.

Ƴan sandan sun jikkata uku daga cikin maharan inda aka tabbatar da mutuwar ɗaya daga ciki daga bisani.

Nansel ya ce tuni zaman lafiya ya dawo yankin kuma kwamishinan ƴak sandan jihar, Umar Nadada ya bada umarnin kamo waɗanda suke da hannu a lamarin.

More from this stream

Recomended