Mutane biyu ne suka ƙone sosai a yayin da wasu da dama suka jikkata a wata gobara da ta kama a wani gidan mai mallakin kamfanin Mobil a jihar Lagos.
Lamarin ya faru ne ranar Alhamis da misali ƙarfe 11: 00 na safe a gidan man dake kusa da Airport Hotel, Ikeja dake kan titin Obafemi Awolowo.
Gobarar ta samo asali daga wata motar ɗaukar iskar gas da ta kama da wuta kana ta bazu ya zuwa sauran sassan gidan man da maƙotan gidaje.
Nosa Okunbor Shugaban sashen hulɗa da jama’a na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, LASEMA ya ce musabbabin da yasa motar mai ɗaukar tan 12 na iskar gas ta kama da wuta.
Ya ce motoci 6 da suka haɗa da na gida da na haya gobarar ta rutsa da su.