Mutane 8 sun mutu a hatsarin jirgin kwale-kwale a Jigawa

Mutane 9 ne suka mutu bayan da wani jirgin kwale-kwale dake dauke da fasinjoji 17 yawancinsu  yara mata kanana ya kife da su a karamar hukumar Taura ta jihar Jigawa.

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA ita ta tabbatar da faruwar haka cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis.

A cewar ofishin hukumar ta NEMA dake Kano mummunan hatsarin ya faru ne a yayin da kwale-kwalen ya kife ana tsaka da tafiya daga kauyen Digawa a karamar hukumar Jahun ya zuwa kauyen  Zangon Maje a karamar hukumar Taura.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru a ranar Lahadi da misalin karfe 07:00 na dare kuma jami’an hukumar sun tabbatar da ceto mutane 8 lokacin da suka isa wurin a yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 9.

More from this stream

Recomended