
Mutane 7 ne suka mutu ciki har da wani matukin jirgin kwale-kwale inda suka nutse a ruwa bayan da jirgin da suke ciki ya kife a jihar Sokoto a ranar Litinin .
A cewar Zagazola Makama dake wallafa bayanai kan sha’anin tsaro mutanen sun gamu da ajalinsu akan hanyarsu ta zuwa kauyen Garin Hussaini daga Sabon Garin Hussaini.
Ya ce jami’an tsaro sun gaggauta zuwa wajen inda suka killace bakin ruwan domin hana jama’a da yan uwan mutanen taruwa a wurin.
Mutanen da suka iya ruwa a garin sun samu nasarar fito da gawarwarkin mutanen inda aka mika su ga yan uwansu domin yi musu jana’iza.
Hatsarin jirgin ruwa abu ne da ya zama ruwan dare a Najeriya musamman a yankin jihohi Sokoto, Kebbi, Kogi da kuma Neja inda ake rasa rayukan dinbin mutane a kowace shekara.