
Mutane aka bada rahoton an jikkata bayan da jami’an rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa yan asalin Birnin Tarayya Abuja da suke gudanar da zanga-zanga a majalisar kasa inda suka bukaci a janye nadin da aka yi wa Mr Solomon Adodo wanda dan asalin jihar Benue a matsayin mamba a hukumar gudanarwar Hukumar Bunkasa Yankin Arewa ta Tsakiya.
Masu zanga-zangar karkashin inuwar kungiyar FCT Youth Stakeholders Forum na bukatar a nada dan asalin Abuja a kwamitin gudanarwar hukumar.
Sai dai a dai-dai lokacin da suke gudanar da zanga sun gamu da fushin jami’an yan sandan a lokacin da suka nemi wuce makadi da rawa.