
Akalla mutane yan kasuwa 37 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa garin Gbajigo-Mudi dake jihar Kwara.
Yan kasuwar na kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako a jihar Niger a ranar Alhamis lokacin da hatsarin ya faru.
Jirgin ruwan da aka ce zai iya daukar mutane 100 ne amma sai aka cika shi fiye da ka’ida.
Har ila yau an alakanta hatsarin jirgin ruwan da karfin igiyar ruwa.
Mahmoud Gbajibo tsohon shugaban karamar hukumar ya tabbatarwa da jaridar The Punch faruwar lamarin a ranar Asabar.
Gbajibo ya ce gawarwarkin mutane 37 aka samu nasarar tsamowa daga kogin a yayin da aka ceto mutane da dama.
” hatsarin kwale-kwalen ya faru da misalin karfe 06:00 na yammacin ranar Alhamis. Yan kasuwar sun tashi daga kasuwar Gbajibo-Mudi inda suke komawa kauyukansu daban-daban a jihar Niger lokacin da hatsarin ya faru,” Gbajibo ya ce.
” Za a iya alakanta hatsarin da daukar mutane a cikin jirgin fiye da ka’ida a yayin da yawa da kuma karfin ruwan shima ya taimaka,”