Mutane 32 sun tsira da ransu a hatsarin jirgin sama a Kazakhstan

Wani jirgin saman fasinja da ya taso daga Azerbaijan zuwa Rasha ya yi hatsari a ƙasar Khazastan

Jirgin ƙirar Embaraer  na kan hanyarsa ta zuwa Grozny babban birnin Chechniya inda ya  ke  ɗauke da fasinjoji 62 da kuma ma’aikata 5.

A cewar hukumomin kawo yanzu an tabbatar da cewa mutane 32 sun tsira da ransu a hatsarin kuma wasun su na cikin mawuyacin hali.

Hukumar lura da sufurin jiragen sama ta ƙasar Rasha ta ce jirgin ya faɗo ne sakamakon karo da ya ci da tsuntsu a sama kuma matukin jirgin ya bukaci yin saukar gaggawa.

Hukumomin ƙasar, Khazastan sun ce tuni aka kafa kwamitin bincike kan hatsarin.

Gwamnatin ta ce tuni ta tura jami’ai zuwa wurin domin su kai ɗauki iyalai da kuma mutanen da lamarin ya rutsa da su.

Shi ma shugaban ƙasar, Azerbaijan, Ilham Aliyev ya katse ziyarar aiki da yake a Rasha domin komawa gida sakamakon hatsarin.

More from this stream

Recomended