
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Niger NSEMA ta ce aƙalla mutane 29 ne suka mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a ƙaramar hukumar Borgu ta jihar.
Hukumar ta bayyana haka ne ta darakta janar na hukumar, Abdullahi Arah a wata sanarwa da ya fitar.
Arah ya ce jirgin na dauke da mutane 90 lokacin da hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11:20 na safiyar ranar Talata a Gusawa dake mazabar Malale.
Ya ce jirgin ya taso ne Tungan Sule dake mazabar Shagunu inda ya ci karo da tsiron bishiya a cikin ruwa akan hanyarsa ta kai mutanen dake ciki garin Dugga gaisuwar ta’aziya.
Shugaban na NSEMA ya tabbatar da cewa ɗaukar mutane fiye da ka’ida ne ya haddasa hatsarin ya kara da cewa mutane 50 aka samu nasarar ceto wa da ransu a yayin da biyu suka ba ce.
“A yanzu da ake bada wannan rahoton an gano gawar mutane. Ana cigaba da aikin ceto da kuma neman mutanen da suka ba ce,” a cewar sanarwar.