
Mutanen da basu gaza 25 ba ne ciki har da yan gida daya su 10 aka tabbatar da sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa a karamar hukumar Shiroro ta jihar Niger.
Rahotanni dake fitowa daga yankin sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne da misalin karfe 02:00 na ranarĀ Asabar lokacin da mutanen suke kan hanyarsu ta zuwa kasuwar mako ta Zumba.
Sarkin Ruwan Zumba, Umar Isa ya yi kiyasin wadanda suka mutu za su kai mutum 25.
Isa ya ce mutanen sun tawo daga garin Guni dake karamar hukumar Munya ta jiharĀ za su je cin kasuwar Zumba dake karamar hukumar Shiroro ta jihar.
Ya ce duk da cewa matukin jirgin shima bai san yawan fasinjojin dake cikin jirgin ba wasu iyalai biyu sun tabbatar da rasa mutane 10 da kuma 5 kowannensu.