
Hukumar FRSC dake kiyaye afkuwar hatsura akan titunan Najeriya ta ce fasinjoji 19 suka mutu a wani hatsarin mota akan hanyar Lokoja zuwa Obajana a jihar Kogi.
Olusegun Ogungbemide mai magana da yawun hukumar ta FRSC a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin ya bayyana cewa mutanen 8 ne suka ji raunuka iri daban-daban a hatsarin.
Ogungbemide ya ce hatsarin da ya faru kusan karfe 06:10 na yamma a Gada Biyu ya rutsa da wata babbar motar kirar Sino Truck da kuma Toyota Hiace dake dauke da fasinjoji 27 manya 22 da kuma kananan yara 5.
Ya ce shugaban hukumar ta FRSC, Shehu Muhammed ya bayyana matukar alhininsa kan hatsarin tare da yin jaje ga iyalan mutanen da suka rasa yan uwansu a hatsarin.
Ya kara da cewa binciken da aka gudanar ya nuna cewa gudun wuce sa’a da kuma kokarin wuce wata motar ba dai-dai ba shi ne musabbabin hatsarin.
Tuni aka binne mamatan da suka mutu bayan da aka yi musu sutura da jana’iza a wani masallaci kamar yadda addinin musulunci ya tanada.