Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake ƙaramar hukumar Ijebu East ta jihar Ogun.

Mutanen dake cikin wata motar ƙirar Hiace mai rijistar namba XA 690 AKU sun ƙone ƙurmus a yayin da wani fasinja guda ɗaya ya tsira da ransa.

Babajide Akinbiyi jami’in hukumar tabbatar da bin dokokin hanya ta jihar Ogun shi ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abeokuta babban birnin jihar.

Hatsarin ya faru ne sakamakon malalar man fetur da aka ɗauko a cikin wata jarka a cikin motar kamar yadda direban motar da ya tsira da ransa da kuma wani shedar gani da ido suka shedawa hukumar.

Akinbiyi ya ce fetur ɗin ya faɗi ya malale lokacin da motar ta shiga gargada har ta kai ga ya  gangara inda salansar motar take  hakan yayi sanadiyar kamawar wuta.

Shugaban ya gargaɗi direbobi da masu ababen hawa da su guji a jiye fetur a cikin jarka.

More from this stream

Recomended