Mutane 16 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ogun

Fasinjoji aƙalla 16 aka bada rahoton sun ƙone ƙurmus a yayin da wasu uku suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a jihar Ogun a ranar Talata.

Hatsarin ya faru ne a wajen rukunin gidaje na Buhari dake kan babban titin Abeokuta zuwa Sagamu.

Wata mota fara ƙirar Da rijistar namba KJA 949 YJ ita ce tayi hatsarin da misalin ƙarfe 01:00 na rana.

Mai magana da yawun hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta ƙasa a jihar Ogun, Florence Okpe ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata.

Ta ce an gaza tantance jinsin mutanen da hatsarin ya rutsa da su saboda yadda suka ƙone ƙurmus.

Okpe ta ɗora alhakin afkuwar hatsarin kan wuta da ta kama a cikin motar da kuma tukwane dake ɗauke da iskar gas da suka yi bindiga a lokacin da hatsarin ya faru.

More from this stream

Recomended