Mutane 16 masu garkuwa da mutane da aikata muggan laifuka sun faɗa hannun ƴan sanda a Abuja

Rundunar yan sandan Najeriya ta kama mutane 16 da ake zargin suna da hannu ayin garkuwa da mutane da kuma aikata wasu manyan laifuka a birnin tarayya Abuja.

Da yake sanar da kama mutanen mai magana da yawun rundunar yan sandan, Muyiwa Adejobi ya ce uku daga cikin mutanen da aka kama ana zarginsu da yin garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a yankin Bwari dake Abuja.

Adejobi ya kara da cewa rundunar yan sandan ta samu nasarar daƙile yinkurin yin garkuwa da mutane ta hanyar bayanan sirri inda ta kama masu shirya yin garkuwa tare da wasu makamai.

“A cikin masu laifin da aka gabatar yau a kwai uku dake zaune a Bwari suna garkuwa da mutane Idris Ishaku mai shekaru 27, Bala Umar mai shekaru 27 da kuma Dahiru Salisu mai shekaru 27 wadanda suke da alhakin jerin garkuwa da mutane da fashi da makami a Bwari dama wasu sassan birnin tarayya Abuja. “sanarwar ta ce.

More from this stream

Recomended