
Mutanen da basu gaza 15 ne ba aka tabbatar da sun mutu wasu kuma biyar suka jikkata a wani hatsarin mota da ya faru akan titin Lapai-Agaie- Bida ƙaramar hukumar Agaie ta jihar Neja.
Hatsarin da da ya faru a ranar Asabar ya rutsa da wata mota ƙirar bass wacce tayi ƙoƙarin wuce wata motar tanka tana tsala gudu.
Kwamandan shiya na hukumar FRSC dake kiyaye afkuwar hatsura a Najeriya, Kumar Tsukam ya tabbatar da faruwar hatsarin a zantawar da ya yi da jaridar Leadership in da ya ce ya faru ne a garin Kusobigi dake kusa da Nami.
Hatsarin mota abu ne da ya zama ruwan dare akan titunan Najeriya inda a duk shekara dubban mutane suke rasa rayukansu.