Mutane 14 ne suka mutu a sakamakon ambaliyar ruwa a jihar Niger

[ad_1]








Garba Salisu, daraktan sashen agaji a hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger ya ce ya zuwa yanzu mutane 14 ne suka mutu sanadiyar ambaliyar ruwa da ta faru a sassa daban-daban na jihar.

A wata tattaunawa da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ranar Asabar, ya ce hukumar ta dauki kwararru da suka iya ruwa su 200 domin su taimaka wajen aiyukan ceto.

Salisu ya roki mazauna jihar da su guji gini kan hanyoyin ruwa kana su daina zubar da shara barkatai domin gujewa illar ambaliyar ruwa.

“Babban abinda nafi tsoro shine yawancin ruwan da ake yi na dare ne lokacin da mutane suke bacci amma mafita ɗaya ce shine samar da muhalli da zai tabbatar da wucewar ruwa ba tare da tsaiko ba.”ya ce

Daraktan ya yi kuma kira ga al’ummomin dake wuraren dake yawan samun ambaliyar ruwa da su kauracewa wuraren na wucin gadi domin kaucewa masifa.




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...