Aƙalla mutane 13 aka bada rahoton sun mutu bayan da wani ramin haƙar ma’adinai ya rufta a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Shugaban karamar hukumar ta Bassa, Joshua Riti ya ce lamarin ya faru ranar 10 ga watan Nuwamba ya ƙara da cewa 7 daga cikin waɗanda suka mutu sun fito daga Bassa.
Wurin haƙar ma’adanan da ya rufta ya yi iyaka da kananan hukumomi Jos north da kuma Jos south.
“Lamari ne mara ɗaɗi saboda waɗannan matasa sun je neman na abinci ne kawai,” a cewar shugaban ƙaramar hukumar.
“Sun fita suyi amfani da karfinsu domin neman abun da za su magance wahalar matsin tattalin arziki da ake fama da shi a ƙasa amma sai suka gamu da ajalinsu,” ya ce.
Shugaban ya kuma miƙa saƙon ta’aziyarsa ga iyalai da ƴan uwan wadanda suka mutu.
Yawancin waɗanda suka mutu matasa ne shekarunsu su ka kama daga 18 zuwa 30.