
Jami’an hukumar LASEMA ta bada agajin gaggawa ta jihar Lagos sun samu nasarar kashe wata gobara da ta kama a wani ginin bene mai hawa 22 dake kan layin Martins a unguwar Lagos Island.
A wata sanarwa ranar 25 ga watan Disamba, Damilola Oke-Osanyintolu darakta janar na hukumar ta LASEMA yayi cikkaken bayani cewa gobara ta fara ci ne a ranar 24 ga watan Disamba ta kuma yadu ya zuwa gine-ginen dake kusa ciki har da wani masallaci amma kuma an samu nasarar shawo kanta.
” A yanzu an samu nasarar shawo kan gobara sakamakon kokarin dukkanin masu kai dauki,” ya ce.
Ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta fara ne daga wani gini dake hawa na 6 kafin daga bisani ta bazu ya zuwa sauran wurare.
Oke-Osanyintolu ya ce manya maza bakwai ne suka samu raunin kuna iri-iri inda aka basu kula gaggawa kafin akai su asibiti . Yi
Ya kara da cewa wasu an bawa wasu mata biyu da kuma maza biyu kulawar gaggawa daga jami’in bada agajin gaggawa.

