
Aƙalla mutane 12 ne aka tabbatar da sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota akan hanyar Benin zuwa Auchi a jihar Edo.
Kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hatsura ta ƙasa, FRSC shiyar Edo, Cyril Mathew wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce hatsarin ya rutsa da wata mota ƙirar Toyota Hiace da kuma babbar mota.
Ya ce hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 05:00 na asubahin ranar Asabar a kusa da shingen binciken jami’an tsaro dake garin Igueviobo.
Ya ce ” Motar ta taso daga Zuba a Abuja inda ta nufi Benin amma taci karo da wata babbar mota da ta nufi Auchi inda dukkanin mutanen cikin motar hayar suka mutu,”
“Ya faru ne da asubahin ranar Asabar dole akwai gajiya a tare da direban da ya taso daga Abuja kuma wataƙila bacci ya ɗauke shi har ya je ya ci karo da babbar motar,”
Ya ce direban babbar motar da kuma yaron motar sun samu nasarar tsira da rayukansu ba tare da sunji rauni ba.