Mutane 10 sun warke daga cutar Coronavirus a Osun – AREWA News

Marasa lafiya 10 da aka tabbatar suna dauke da cutar Coronavirus aka sallamesu daga asibiti bayan da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa basa dauke da cutar.

Gwamnan jihar Gboyega Oyetola shine ya sanar da haka a wurin wani taron manema labarai ranar Asabar.

Yawan masu ɗauke da cutar Corona a jihar ya karu sosai bayan da wasu yan jihar suka dawo daga kasar Kodebuwa.

Mutane 18 cikin wadanda suka dawo su 127 aka samu suna dauke da cutar.

Bayan sallamar mutane 10 da suka warke yanzu yawan wadanda suka warke daga cutar a jihar ya zama 11.

More from this stream

Recomended