Musulmi sun yi rokon ruwa ranar Sallah

[ad_1]

Muslims pray in Sydney at the Lakemba mosque

Hakkin mallakar hoto
Lebanese Muslim Association

Image caption

Dubban mutane ne suka halarci sallar Idi a Sydney

Kimanin Musulmin Australia 30,000 ne suka taru a birnin Sydney ranar Talata inda suka yi sallar rokon ruwa sakamakon mummunan farin da ba a taba fuskantar irin sa ba a kasar.

Masallata daga manyan masallatai 16 ne suka hadu wuri guda “domin nuna goyon baya da ba da hadin kai” ga manoma da sauran mutanen da farin ya shafa.

An yi sallar ne lokacin da aka gudanar da babbar sallah sannan aka yanka dabbobi.

An kaddamar da wata gidauniyar tallafa wa manoman da farin ya shafa.

Kungiyar Musulmi ‘yan kasar Lebanon da ke masallacin Lakemba na yammacin Sydney ce ta kaddamar da gidauniyar.

“A matsayinmu na ‘yan uwa daya ‘yan kasar Australia, muna ganin ya kamata mu bayar da tamu gudunmawar da goyon baya ga mabukata,” in ji shugaban kungiyar Samier Dandan.

“Wannan ne lokacin da ya kamata mu hada kai mu tallafawa wadanda ke cikin mawuyacin hali.”

Hakkin mallakar hoto
LMA

Image caption

An yi sallar rokon ruwan ce a masallacin Lakemba da ke yammacin Sydney

Daraktan kungiyar, Ahmad Malas, ya shaida wa BBC kowa ya ji dadi lokacin da aka kaddamar da gidauniyar.

Ya kara da cewa ana yin sallar rokon ruwa ce idan ana kamfar ruwan sama.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Manoma na fuskantar matsala wurin shayar da dabbobinsu

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...