Musulmi  a Fadin Duniya Na Harmar Karamar  Sallah

Musulmi a fadin duniya na shirin shagulgulan zagayowar daya daga cikin bukukuwansu mafiya girma duk kuwa da kalubalen cutar corona. Bukin na karamar Sallah ta Eid al-Fitr na tsawon kwanaki uku ana kyautata zaton za a fara shi ne daga yau Asabar ko kuma gobe Lahadi, wanda ke tabbatar da karewar watan azumi na Ramdan ga Musulmin duniya masu yawan kimanin biliyan 1.8. Bisa al’ada wannan bukin ya hada da tafiye-tafiye, ziyarce ziyarce da kuma haduwa a ci hadadden abinci, wadanda duk za a takaita su wannan karon saboda hukumomi na kokarin dakile sake barkewar cutar.

Wasu kasashen, ciki da Turkiyya da Iraki da Jordan, za su kafa dokar hana fita a tsawon lokacin bukin na Sallah. A Saudiyya, inda nan ne birane masu tsarki na Makka da Madina su ke — za a bar mutane su fita daga gidajensu ne kawai idan za su sayo ko magunguna.

Kai ko ma a kasashen da su ka sake bude harkokin sosai, durkushewar tattalin arzikin da ya biyo bayan kulle da aka yi na makonni da dama na neman rage ma bukin Sallar armashi.

An sassauta tsaurin akasarin matakan da aka dauka a Birnin Kudus, to amma masallacin Al-Aqsa – wanda shi ne na uku a tsarki a Musulunci – zai cigaba da kasancewa a rufe har sai bayan karamar Sallar. ‘Yan tireda da ke Tsohon Birnin, wanda ya kasance babu masu zuwa ziyarar harkokin ibada da na yawon bude ido, na kokawa da tasirin kullen da aka yi na tsawon makonni.

More News

An fara rushe wasu gine-gine 500 a kasuwar Karmo dake Abuja

Hukumar FCTA dake kula da birnin tarayya Abuja ta fara rushe gine-gine sama da 500 da aka yi ba bisa ka'ida ba a kasuwar...

Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu ya tarbi shugaban kasar Senegal Bassirou Faye a fadar Aso Rock Villa, a ziyarar da Faye ya...

NEMA ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo dasu gida daga ƙasar Chad

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA ta ce ta karɓi ƴan Najeriya 150 da aka dawo da su bayan da su ka maƙale...

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙi amincewa da ₦48,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Taron zaman ganawa da ƴan kungiyar ƙwadago da gwamnatin ta tarayya ta kira  ya tashi babu shiri bayan da wakilan kungiyar ƙwadago suka fice...