
Asalin hoton, Getty Images
Wannan mukala ce daga Imam Murtadha Muhammad Gusau, babban limamin masallacin Nagazi-Ovete da ke Okene na jihar Kogin Najeriya, ya rubuta kan sha’anin sabuwar shekarar Musulunci musamman abin da ya shafi bukukuwa da taya murnar shigowarta.
A yau ne dai 1 ga watan Muharram 1442 bayan hijrar Annabi Muhammad (SAW) daga Makkah zuwa Madina.
Me malamai suka ce kan sabuwar shekarar Musulunci?
Asalin hoton, Imam Murtada
Imam Murtada Muhammad ya ce “abin lura shi ne sabanin tsakanin Musulmi kan shekarar Musulunci bai kamata ta zama hanyar rikici ba.”
Da sunan Allah mai rahama, mai jin ƙai.
Jama’ar Musulmi, batun Hijirah ba ƙaramin al’amari ba ne a wurin al’ummar Annabi Muhammad (SAW). Don haka ya zama wajibi a kan duk Musulmai su dauke shi da matukar muhimmanci.
Kamar yadda kuka sani, a duk lokacin da muka doshi shiga sabuwar shekarar Musulunci ta hijirah, to za mu ga ana yawaita tattauna maganganu muhimmai a kan ta, wani lokaci kuma a yi ta hayaniya.
Daga cikin abubuwan da ake yawan tattaunawa a kai cikin irin wadannan lokuta da ake fuskantar shigowar sabuwar shekarar Musulunci, akwai hukuncin yin bukukuwan sabuwar shekara. Shin ya halatta ko bai halatta ba? Shin bidi’ah ne ko Sunnah ne?
A gaskiya cikin abun da na karanta, kuma na fahimta shi ne, wannan mas’ala ce da magabata na can baya sosai ba su tattauna a kan ta ba, (ma’ana) wata tattaunawa ta musamman. Sai dai Malaman da suka zo daga baya-bayansu, su ne suka tattauna a kan ta. Misali:
Imam As-Suyudi – Allah ya jikan sa da rahama – ya ambace ta a cikin littafinsa mai suna: “وصول الأماني بأصول التهاني” a cikin juzu’i na daya, da ke cikin littafinsa “الحاوي للفتاوي”, ga abin da yace:
“Imam Al-qamuli ya ce, ban ga mutanenmu (ma’ana mazhabin Shafi’iyyah) sun yi wata magana ba a kan taya murnar Idi, ko shekaru, ko watanni, kamar yadda mutane suke yi ba.
Amma na gani a cikin fa’idodin da aka cirato daga Zakiyyuddini Abdul’azim Al-munziri, cewa lallai babban malami Abul-Hasan Al-makdisi an tambaye shi game da taya murna a farkon shigar watanni, da shekaru, shin Sunnah ne ko bidi’ah? Sai ya bada amsa kamar haka:
“Mutane ba su gushe ba suna sabani a kan haka, sai dai ni ina ganin halal ne kawai, ba Sunnah ba ne ba bidi’ah ba. Haka ma Sharaf – Algazzi ya cirato a cikin sharhin littafin Al-minhaj, kuma bai kara komai a kai ba.” [Duba Al-Hawi, Juzu’i na 1, shafi na 82]
Haka an ruwaito Imam Ahmad – Allah ya jikansa da rahama – yana cewa a game da taya murnar idi ma, ba sabuwar shekara ba:
“Ni ba na fara taya wani murnar idi, amma idan wani ya fara min, to ina mayar masa.”
Sai Shaikhul Islam Ibn Taymiyyah, Allah ya jikansa da rahamarsa, ya ce:
“Imam Ahmad ya yi haka ne saboda mayar da gaisuwa tilas ne, amma fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umurni da ita ba, sannan kuma ba a hana yi ba, wanda ya aikata ya yi koyi, wanda kuma ya ki ya yi, shi ma ya yi koyi.”
A karkashin haka, ina iya cewa: taya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci, halal ne a wurin wasu malamai, wanda ba ya da alaka da ibadah, wato al’ada ce ta mutane su taya junansu murna ba don suna tsammanin wata lada daga wurin Allah ba.
A wurin wasu malamai kuwa ba a yi, kuma suna ganin cewa bidi’ah ce, matukar an alakanta shi da addini, wato idan mutane suna ganin cewa abun da suke yi wani abu ne da addini ya yi umurni da a yi shi.
Wadannan Malamai, kuma suna kafa dalili da cewa, magabata ba su yi ba.
Sannan kamar yadda ya zo a tarihance, Imam Hafizul Maqrizi ya ba da labari a cikin littafinsa mai suna “Al-khutat” cewa:
“Sarakunan gwamnatin Ubaidiyyah ta ‘yan Shi’a a Misrah, su ne suka fara gudanar da bikin sabuwar shekara.”
Sannan daga cikin abun da ya kamata mu lura da shi a nan shi ne, a Musulunci, bayan ranakun Sallah karama da Sallah babba, ba wata rana a shekara da aka umurci Musulmi su yi riko da ita a matsayin ranar bikin shekara.
Duk da yake akwai wasu ranaku masu tarihi a Musulunci, irin ranar hijirah, ranar yakin badar, ranar sulhun hudaibiyyah, ranar fathu Makkah da sauransu, amma Musulmin farko ba su yin bikin tunawa da daya daga cikin wadannan ranakun ko wasunsu.
A karkashin haka ne Malamai da dama suka ba da fatawa a kan cewa bikin murnar sabuwar shekarar Musulunci bidi’ah ne, ba shi da asali a cikin addinin Allah, don haka wajibi ne ga Musulmi su bar shi.
Sannan wani karin abun da ya kamata mu fahimta a nan shi ne, cewa halal ne taya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci a wurin wasu malamai, ba yana nufin halatta taya wadanda ba musulmi ba murnar shiga sabuwar shekararsu ta miladiyyah, kamar yadda Imam Ibnul-Qayyim yayi bayani a cikin littafinsa mai suna, “أحكام أهل الذمة”, a inda yake cewa:
“Amma taya murna da abubuwan alamomin kafirci, wadanda suka kebanta da shi, haramun ne, babu sabani a kan haka tsakanin malamai. Kamar mutum yace: barka da idi, ko makamancin haka.”
Tsokaci akan wasu abubuwa da wasu mutane ke yi
1. Baya cikin Sunnah tara mutane domin yin bikin sabuwar shekarar Musulunci, har a sauke Alkur’ani mai girma, ko ayi wasu addu’oi, ko a bayar da hutun aiki akan haka.
2. Ba kawai sabuwar shekarar Musulunci ba ne abun murna, a’a me za’a gabatar a cikinta shine abun tambaya kuma shine abun ayi murna ko ayi kuka.
3. Akwai banbanci tsakanin taya murnar sabuwar shekara, da daukar haka wato: shiga sabuwar shekarar a matsayin ranar biki, da haduwa, da shagulgula.
Darussa guda biyar da al’ummar Musulmi za su koya game da Hijirah
1. Hijirah na karantar da mu cewa, Allah Subhanahu wa Ta’ala ba ya bukatar kowa domin addininsa ya ci gaba.
Da duk mutanen duniya, kowa zai cire hannunsa wurin taimakon addinin Allah, to mu sani, addinin zai ci gaba, domin Allah ya yi alkawarin zai kare addininsa.
Mutane ba su taba tsammanin cewa Annabi Muhammad (SAW) zai tsira daga sharri da makircin da makiyansa suke kulla masa ba a Makkah, amma Allah ya kubutar da shi, ta hanyar yin hijirah daga Makkah zuwa Madinah.
Duk abun da suka kulla, Allah ya rusa shi, ya bata shi kuma ya lalata shi. Don haka, kenan idan muka taimaki addinin Allah kawunanmu muka taimaka!
2. Hijirah tana koyar da mu cikakken imani da Allah, da dogaro gare shi, cewa lallai za ya kubutar da mu, kuma za mu tsira daga dukkan halin damuwa da kunci da muka samu kan mu a ciki.
A hanyarsu ta yin hijirah, Annabi Muhammad (SAW) da abokinsa kuma sahabinsa, wato Abubakar As-Siddiq, sun shiga cikin halin damuwa da cewa lallai makiyansu za su riske su, su kama su, su halakar da su.
Amma da yake suna da cikkaken dogaro da tawakkali ga Allah, sai ya kubutar da su, makiya ba su ci nasara wurin kama su ba.
3. Hijirah tana koyar da mu yin cikakkiyar biyayya ga Allah, a duk lokacin da ya umurce mu da yin wani abu, kuma ko da ba mu gane hikimar da ke cikin umurnin ba.
Domin Allah ya umurci Annabi Muhammad (SAW), da ya yi hijirah, ya bar garinsa na haihuwa. Ba tare da wani musu ba, Annabi ya bi umurnin Allah.
4. A cikin hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makkah zuwa Madinah, za mu fahimci wani darasi muhimmi, wanda yake koyar da mu cewa lallai komai tsanani, to sauki yana nan zuwa da yardar Allah.
Dubi shekaru goma sha uku da Annabi (SAW) ya yi a Makkah cikin cutarwa da ukubar kuraishawa masu tsananin adawa da shi.
Amma da ya daure, ya yi hakuri, ya fahimci cewa lallai bayan tsanani sauki yana zuwa, daga karshe sai ya ci nasara a kan dukkanin makiyansa.
Tun daga lokacin da ya yi hijirah zuwa Madinah, sai Allah ya kawo sauki. Don haka duk halin da bawa ya samu kansa a ciki na tsanani, na jarrabawa, to ya sani da ikon Allah sauki yana nan zuwa!
5. Hijirah tana koyar da al’ummar Musulmi ‘yan uwantakar Musulunci.
Duk inda ka samu Musulmi a duniya, to ɗan’uwanka ne. Shin baki ne, fari ne, ja ne, duk addinin Allah bai san da wannan bambancin ba.
Dukkaninmu ‘yan uwan juna ne. Don Allah dubi yadda mutanen Makkah suka baro garinsu ba tare da sun dauko komai ba.
Mutanen Madinah suka karbe su a matsayin ‘yan uwansu. Suka raba komai da suke da shi suka ba su rabi: gida, mata, dukiya da sauransu.
Kammalawa
Daga karshe, to koma dai menene, ni ina ganin tun da ya kasance wannan mas’ala ce da al’ummah suka sabawa juna a kan ta, bai kamata ta zama sanadiyyar rarrabuwar mu ba, bai kamata mu kasance muna kafirta junanmu a kan ta ba, ko fada da juna, ko yin wata hayaniya marar kyawu da junanmu a kan ta ba.
Har kullum, idan kana da wani ra’ayi, ko wata fahimta da kake ganin su ne mafi zama daidai, to yi kokari ka fahimtar da dan’uwanka Musulmi cikin ruwan sanyi, kuma ta hanyar ilimi, yadda zai fahimce ka, ba tare da wata tsangwama ko cin mutunci ba!
Allah nake roko ya taimake mu, ya karawa rayuwarmu albarka, ya sa mu amfana da ita, kuma ya sa mu cika da imani, amin.