Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce tana bibiyar wadanda suka yi garkuwa da wasu masu hakar ma’adanai 16 a kokarin da take na kubutar da su.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, DSP Sabo Audu lokacin da yake zantawa da jaridar Daily Trust ta wayar tarho ya ce ” masu garkuwar sun tuntubi iyalan mutanen domin tattauna batun biyan kudin fansa ya yin da suke haka,mu kuma muna bibiyarsu.”
Idan za a iya tunawa wasu mutane 16 da aka bayyana da masu hakar ma’adanai inda shida daga cikin sun fito daga tsatso daya sun fada hannun masu garkuwa da mutane akan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.
Shugaban kungiyar Birnin-Gwari Vanguards for Security and Good Governance, Abdullahi Ibrahim Nagwari a wata sanarwa da ya fitar jiya ya ce sun tabbatar da faruwar lamarin kuma masu garkuwar sun bukaci a biya su miliyan daya akan kowane mutum a matsayin kudin fansa.
Shugaban ya nemi gwamantin tarayya da ta kaddamar da yaki kan mutanen da ya kira yan ta’adda da suka addabi yankin.
Garkuwa da mutane a yankin na Birnin Gwari abune da ya zama ruwan dare kuma ga dukkan alamu hukumomi sun gaza wajen shawo kan lamarin.