Mummunan Hatsarin Mota Ya Hallaka Daliban UNIJOS a Kan Titin Zaria

Akalla daliban Jami’ar Jos (UNIJOS) takwas sun rasu da safiyar Alhamis, 11 ga Disamba, bayan wata babbar tirela ta kwace hanya wa direban inda ya buge bas ɗin da ke dauke da su a kan titin Zaria Road, cikin birnin Jos na Jihar Filato.

Rahotanni daga wajen da lamarin ya faru sun nuna cewa direban bas ɗin ma ya mutu nan take, yayin da dalibai biyu da suka tsira aka garzaya da su zuwa asibiti domin kulawa.

Wani shaidan gani-da-ido ya bayyana cewa daliban suna komawa gida ne bayan wani yawo da suka yi a daren, inda suke cikin bas guda daga cikin motocin haya biyu da suka dauka, lokacin da tirelan da ke tafe da gudu ya yi amfani da birki kuma ya kasa tsayawa ya buge su a kusa da filin wasa na Zaria Road Stadium.

More from this stream

Recomended