MSMEs Survival Fund: Gwamnatin Buhari ta ce mutum fiye da 100,000 sun amfana da tallafin

Mai kosai a Abidjan

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi nisa wajen aiwatar da shirinta na tallafa wa kananan masana’antu da masu sana’ar hannu da Naira biliyon saba’in da biyar, kasancewar fiye da mutum 100,000 ne suka ci gajiyar shirin.

Gwamnati na ba da tallafin da nufin rage musu jikkatar da suka yi daga annobar korona.

Gwamnatin Najeriyar ta bayyana cewa a kalla kamfanoni fiye da 25,000 ne suka samu tallafin, wadanda suka hada da kananan masana`antu da makarantun kudi ko masu zaman-kansu, wadanda ke kunshe da ma`ikata fiye da mutum 100,000 da suka fara samun tallafin.

Tallafin, wanda aka kashi gida uku, ma`aikatar da sauran hukumomin da aikin ke wuyansu sun dukufa wajen kaiwa ga kowane rukuni.

Minista a ma`aikatar ciniki da kasuwanci ta kasar, Ambassada Maryam Yalwaji Katagum ta yi wa BBC karin bayani:

“Mun riga mun fara biyan albashi na tallafi na wata uku-uku, an fara biyan watan farko. Kuma mutum ya fi 100,000 wanda aka fara biya.”

Kimanin Naira biliyan 75 gwamnatin Najeriyar ta ware don tallafa wa kananan masana`antu da kuma masu sana`ar hannu.

Gwamnatin na harin tallafa wa masu sana`ar hannu 333,000 ne a kasa baki daya.

Ana kuma sa ran a kalla mutum 9,000 ne daga kowace jiha cikin jihohin 36 da ke kasar za su amfana, inda wasu za su samu naira dubu talatin-talatin, wasu kuma naira dubu hamsin-hamsin.

Duk da cewa gwamnati ta ce an kebe wa kowace jiha kasonta, kukan da ke fitowa daga wasu jihohi shi ne, an rufe shafin intanet da masu bukatar tallafin za su shiga domin cika fom, alhali kuma adadin wadanda suka cika bai kai yawan mutanen da aka kebe musu ba.

Sai dai shugaban hukumar da ke bunkasa kanana da matsakaitan masana`antu ta Najeriya, Dr Dikko Umaru Radda ya ce sun saurari kukan nasu:

“Duk jihar da ba ta cika ka’idarta ba, kudinta na nan a ajiye kamar yadda shugaban kasa ya bayar da umarni.”

Ya kara da cewa, “Za mu sake bude mu su shafinmu na yanar giz domin su sake shiga domin kowa ya kammala matakan da suka kamata domin kuma su sami tallafin da suke bukata.”

A Najeriyar, gwamnatoci kan kaddamar da irin wannan tsari na tallafa wa al`uma, amma sau tari matsaloli irin su banbancin siyasa ko bangaranci kan nakasa shi, inda ake zargin cewa a karshe tallafin kan kare a hannun wasu da ba sa bukata, ko masu matacciyar zuciya.

Sai dai gwamnati ta ce an tsara neman tallafin ne ta intanet domin a kamanta adalci ta yadda kowa zai gabatar da bukatarsa ba tare da kama-kafa ko sanin wani ba.

(BBC Hausa)

More News

Jihar Neja Ta Yi Rajistar Mutane 289 Da Suka Kamu Da Cutar Amai Da Gudawa, 17 Sun Mutu

Wata annobar cutar amai da gudawa a Jihar Neja ta yi sanadin mutuwar mutane 17 tare da kama mutane 289 a kananan hukumomi 11...

An ƙona sakatariyar ƙananan hukumomi 2 a jihar Rivers

Wasu da ake kyautata zaton ɓatagari ne sun ƙona wani sashe na sakatariyar ƙananan hukumomin Eleme da Ikwerre dake jihar Rivers. Ƙona ginin na zuwa...

Ƴanbindiga sun hallaka wani shugaban APC a Kebbi

Wasu ‘yan bindiga sun harbe Bako Bala, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Suru a jihar Kebbi, a yayin wani yunkurin yin garkuwa da...

Kotu ta hana VIO kamawa, tsare motoci ko cin tarar direbobi a kan hanya

Justis Evelyn Maha ta Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayar da umarni da ya hana Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa, wanda aka...