
Hatsarin mota ya rutsa da motar babban hafsan sojan Najeriya, Tukur Yusuf Buratai.
Lamarin ya faru ne akan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wajejen Jere.
Hedkwatar rundunar sojan Najeriya ce ta bayyana faruwar hatsarin cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.
Sanarwar ta ce wata mota ce tayi taho mugama da motar babban hafsan.
Buratai dai baya cikin motar lokacin da abun yafaru amma dogarinsa dake ciki ya samu raunuka kuma an kai shi asibit inda likitoci ke cigaba da kulawa da shi.