Connect with us

Hausa

Mohammed bin Salman: Yariman Saudiyya na neman kyakkyawar alaƙa da Iran

Published

on

Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Yarima Mohammed ya ce Saudiyya ba ta son “batun Iran ya zama mai wahala”

Yarima mai jiran gado a Saudiyya Mohammed Bin Salman ya ce kasarsa na son ƙulla kyakkyawar danganta da babbar kasar da suke hammaya da ita Iran.

Yariman ya shaida wa kafar talabijin ta Al Arabiya cewa kasarsa na son Iran ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya.

Kalaman Yariman na zuwa ne kwanaki bayan wasu rahotanni sun ambato cewa wasu manyan jami’an gwamnatocin kasashen biyu sun tattauna a asirce a kasar Iraƙi, domin su shirya.

Majiyoyin Saudiyya sun musanta rahotannin. Amma Ma’aikatar harkokin wajen Iran ba ta tabbatar ba kuma ba ta musanta batun ba, tana mai cewa “kofar tattaunawarmu a kullum a buɗe take.”

Kasashen biyu da ke gwagwarmayar mamaya da nuna ƙarfin faɗa a ji a Gabas Ta Tsakiya, sun yanke hulɗa a shekarar 2016 lokacin da masu zanga-zangar Iran sun kai hari kan ofishin difilomasiyyar Saudiyya bayan hukuncin da masarautar ta yanke wa wani malamin Shi’a da ake girmamawa.

Yariman Saudiyya ya jaddada cewa kasarsa na da matsala da “halayyar Iran marar kyau” inda ya yi nuni da shirinta na makaman nukiliya, da ƙaddamar da makamai masu linzami, da kuma taimaka wa “haramtattaun ƙungiyoyi masu gwagwarmaya da makamai.”

Ya ce Saudiyya na aiki tare da aminanta kasashen yankin gabas ta tsakiya da kuma ƙasashen waje domin gano bakin zaren warware waɗannan matsaloli.

Ƙasar Saudiyya, wacce ke ɗaukar kanta a matsayin jagoran ƙasashen Musulmi mabiya Sunni, ta shafe shekaru da dama cikin faɗi tashin ganin ta kasance ita ce uwa a ɗaukacin yankin.

Amma, a shekarun bayan nan, gabar da ke tsakaninta da Iran ta ƙara ta’azzara sakamkon yaƙe-yaƙe da ƙungiyoyi masu goyon bayansu ke yi faɗin yankin Gabas Ta Tsakiya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,
Saudiyya da Iran na goyon bayan ɓangarorin da ke rikici a Yemen

A ƙasar Yemen, ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta akasarinsu kasashen Larabawa ne mabiya Sunni da ke goyon bayan dakarun gwamnati a yaƙin da suke yi da mayaƙan Houthi da Iran ke mara wa baya tun a shekarar 2015.

Kasar Iran ta musanta cewa tana yin fasakwaurin makamai zuwa ga ‘yan tawayen na Houthi, da suka durfafi kaddamar da hare-harensu na makamai masu linzami, da kuma jirage marasa matuka a kan biranen kasar ta Saudiyya da wuraren ayyukan hakar man ta.

Saudiyya kuma na zargin Iran da yin katsalandan a kasashen Labanon da Iraƙi, inda mayakan sa-kai na Shi’a da ke samun goyon bayan Iran suka yi ƙarfi ta fuskar soja da siyasa ta hanyar kai hare-hare ga jiragen ruwan dakon mai a Tekun Fasha da kuma kai hare-hare ga cibiyoyin man Saudiyya.

Saudiyya kuma na adawa da yarjejeniyar 2015 da ta taƙaita shirin nukiliyar Iran, kuma ta goyi bayan shawarar da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin watsi da ita da mayar da takunkumin tattalin arziki shekaru uku da suka gabata.

Iran, wacce ta rama ta hanyar keta muhimman yarjejeniyar nukiliya, a yanzu haka tana tattaunawa kai tsaye tare da gwamnatin Shugaba Joe Biden kan yadda za a farfaɗo da yarjejeniyar.

A cikin hirar da aka yi da shi a kafar talabijin a daren Talata, Yarima Mohammed ya ce Saudiyya ba ta son “halin da Iran ke ciki ya kasance mai wahala”.

“Daga ƙarshe, Iran makwabciya ce kuma duk abin da muke fata shi ne a samu kyakkawar alaƙa.

“A karshen wannan rana, Iran kasa ce makwabta kuma duk abin da muke fata shi ne a samu kyakkyawar alaka.

“Matsalarmu ita ce “halayyar Iran marar kyau” daga shirinta na makaman nukiliya, da goyon bayan da take ba ƙungiyoyi masu makamai da makamanta masu linzame.”

Kalaman na Yarima Mohammed, wanda ake ganin shi ke gudanar da mulkin Saudiyya, sun sha bamban da na shekarun baya. A 2018, ya kwatanta Jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da Adolf Hitler.

Da aka tambaye shi game da yaƙin Yemen, wanda ya haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce shi ne mafi munin rikicin jin-ƙai a duniya,Yariman ya ce babu wata kasa da ke son mayaƙa masu ɗauke da makamai a kan iyakokinta.

Ya bukaci ƴan tawayen Houthis, wadanda suka yi watsi da tayin tsagaita buɗa wutar da Saudiyya ta gabatar a watan da ya gabata, da su “zauna kan teburin tattaunawa” don nemo hanyoyin da za su “tabbatar da buƙatun mutanen Yemen da na yankin.”

Yariman ya kuma yi watsi da duk wani bambancin ra’ayi tsakanin ƙasarsa da sabon shugaban Amurka a hirar.

Mr Biden da ke neman sake shiga yarjejeniyar Iran ya janye goyon bayan Amurka ga hare-haren da Saudiyya ke jagoranta a Yemen, yana mai sukar lamirin ƴancin ɗan Adam na Saudiyya da rahoton da ya fitar na leƙen asirin Amurka wanda ya tabbatar da hannun Yarima mai jiran gado a kisan da aka yi wa ɗan jaridar Jamal Khashoggi a 2018. Yariman ya musanta cewa yana da hannu.

“Mun fi sama da kashi 90 na yarjejeniya da gwamnatin Biden kan abin da ya shafi buƙatun Saudiyya da Amurka, kuma muna ƙoƙarin ƙarfafa wadannan bukatun,” in ji Yarima Mohammed. “Babu kokwanto cewa Amurka ƙawarmu ce.”

(BBC Hausa)

Continue Reading
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending