Ministocin kasar Ghana 2 sun mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu

Edward Boamah ministan tsaron kasar Ghana da kuma Ibrahim Mohammed ministan muhalli na kasar na daga cikin mutane 8 da aka tabbatar sun mutu a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu da faru a ranar Laraba.

Jirgin mallakin rundunar sojan kasar ya yi hatsari ne a yankin Ashanti dake kudancin kasar.

Jirgin kirar Z-9 ya taso ne daga Accra babban birnin kasar kuma an daina jin duriyarsa bayan wani lokaci da tashinsa akan hanyarsa ta zuwa Obuasi wani gari da ake hakar gwal a kudancin kasar.

fasinjoji 5 ne a cikin jirgin da kuma ma’aikata 3.

Julius Debrah shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar ya tabbatar da faruwar hatsarin inda ya ce shugaban kasa, John Mahama ya bayar da umarni a yi kasa da tutocin kasar domin nuna alhini.

More from this stream

Recomended